Luke 9

1Ya kira almajiransa goma sha biyu, ya ba su iko su fitar da kowanne irin aljani, su kuma warkar da cututtuka daga mutane. 2Ya aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.

3Ya ce masu, “Kada ku dauki komi tare da ku domin wannan tafiya. Kada ku dauki sanda, ko jakar matafiyi, ko gurasa, ko kudi - Kada ma ku dauki taguwa biyu. 4Dukan gidan da ku ka shiga, ku zauna a gidan har zuwa lokacin da za ku tafi daga wannan yankin.

5Dukan wadanda ba su marabce ku ba, sa’adda ku ke barin wannan gari, ku karkabe kurar kafufunku a matsayin shaida a kansu.” 6Daga nan sai almajiran suka tafi zuwa cikin kauyuka, suka yi ta shelar bishara, su na warkar da mutane a ko’ina.

7Ana nan Hirudus, mai mulki, ya ji labarin dukan abubuwan da su ke faruwa. Ya yi mamaki saboda wadansu mutane suna cewa Yahaya mai yin Baftisma ne ya sake dawowa da ransa. 8Wadansu kuma suna cewa, annabi Iliya ne ya sake bayyana, wadansu kuma suna cewa daya daga cikin annabawa na da can ne ya sake bayyana da rai. 9Hirudus ya ce, “Ba zai yiwu Yahaya ne ba, domin na datse masa kai. To, wanene wannan da ni ke jin wadannan abubuwa a kansa?” Daga nan sai ya cigaba da neman hanyar da zai ga Yesu.

10Sa’adda manzannin suka dawo daga tafiyarsu, suka gaya wa Yesu dukan abubuwan da suka yi. Daga nan sai ya dauke su domin su tafi tare da shi zuwa garin Baitsaida. 11Amma sa’adda taron suka ji inda Yesu ya tafi, sai suka bi shi can. Ya marabce su ya yi masu jawabi a kan mulkin Allah, kuma ya warkar da wadanda su ke bukatar warkarwa.

12Da yake yamma ta fara yi, sai almajiransa goma sha biyu suka zo suka ce da shi, “Idan ka yarda ka sallami wannan babban taron mutane dominsu shiga cikin kauyuka, da ke kewaye da gonaki, dominsu sami abinci da wuraren da za su kwana, da yake mu na nan a wurin da ba kowa.” 13Amma sai ya ce da su, “Ku ba su abin da za su ci.” Suka amsa masa, “Dukan abin da muke da shi shine, ‘Yan dunkulen gurasa biyar da ‘yan kifaye guda biyu, ba za mu iya zuwa mu sawo abincin da zai ishi mutanen nan su duka ba.” 14Mutanen da suke wurin sun kai kimanin mazaje dubu biyar. Sai Yesu ya ce da almajiran, “Ku ce da mutanen su zauna kungiya-kungiya, mutane hamsin a kowacce kungiya.”

15Sai almajiran suka yi haka, dukan mutanen suka zauna. 16Ya dauki dunkulen gurasan guda biyar, da kifin guda biyu, yana dubawa zuwa sama ya albakarce su, sa’annan ya gutsuttsura, ya ba almajiran domin su rarraba wa mutane. 17Dukansu suka ci kowa ya koshi. Daga nan almajiran suka tattara sauran abin da ya rage, har kwanduna goma sha biyu suka cika!

18Wata rana Yesu yana yin addu’a shi kadai, sai almajiransa suka zo sai ya tambaye su, “Wa mutane suke cewa da ni?” 19Suka amsa, “Wadansu suna cewa, Yahaya mai yin Baftisma, wadansu suna cewa kai annabi Iliya ne, har yanzu wadansu suna cewa kai wani cikin annabawa na da can ne ya dawo da rai.”

20Ya tambaye su, “Ku fa? Wa kuke cewa da ni?” Bitrus ya amsa, “Kai Almasihu ne wanda ya zo daga wurin Allah.” 21Sai Yesu ya gargade su da karfi, kada su gayawa kowa haka tukuna. 22Sa’annan ya ce, “Dan Mutum dole ya sha wahalar abubuwa da yawa; dattawa za su ki shi da manyan fristoci da marubuta, sa’annan za a kashe shi. Bayan kwana uku, za a tashe shi da rai.”

23Sai ya ce da su duka, “Dukan wanda ya ke so ya biyo ni, dole ne ya yi musun kansa, ya dauki gicciyen sa kulluyomin, ya biyo ni. 24Dukan wanda yake so ya ceci ransa, za ya rasa shi, amma dukan wanda ya ba da ransa domina, za ya cece shi. 25Wacce riba mutum zai samu idan ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa?

26Dukan wanda yake jin kunya ta da magana ta, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa, sa’adda ya dawo cikin darajarsa da darajar Uba da ta mala’iku masu tsarki. 27Amma ina gaya maku wannan tabbas, wadansu cikinku da ke nan tsaye, ba za su mutu ba sai sun ga mulkin Allah.”

28Kwana takwas bayan Yesu ya fadi wadannan kalmomi, sai ya dauki Bitrus da Yahaya da Yakubu, ya hau kan dutse domin ya yi addu’a a can. 29Sa’anda ya ke yin addu’a sai yanayin fuskar sa ya canza sosai, tufafinsa kuma suka yi sheki da haske kamar walkiya.

30Nan da nan sai ga mutane biyu suna magana da shi, wato Musa da Iliya. 31Suka bayyana da daraja kewaye da su, suka yi magana da Yesu a kan tafiyarsa wadda za ta zo ba da dadewa ba a cikin Urushalima.

32Bitrus da almajiran da suke tare da shi barci mai nauyi ya dauke su. Sa’adda suka farka sai su suka ga daukakar Yesu; kuma suka ga mutanen su biyu da ke tsaye tare da shi. 33Sa’adda Musa da Iliya suke shirin su bar wurin Yesu, sai Bitrus ya ce, “Ya shugaba, ya yi kyau da muke a nan. Zai yi kyau mu yi runfuna uku, daya dominka, daya domin Musa, daya kuma domin Iliya.” Amma hakika bai san abin da ya ke fadi ba.

34Sa’adda yake fadin haka sai wani girgije ya zo ya rufe su. Sai suka ji tsoro sa’adda girgijen ya kewaye su. 35Sai ga wata murya daga cikin girgijen tana cewa, “Wannan Dana ne wanda na zaba, ku ji shi.” 36Sa’adda muryar ta gama magana, Yesu yana nan shi kadai. Suka yi shiru ba su iya cewa kome ba a kan abin da suka gani a kwanakin nan.

37Washe gari, da suka sauko daga kan dutsen, sai taron mutane da yawa suka zo wurinsa. 38Nan da nan, wani mutum daga cikin taron mutanen ya yi magana da karfi, “Mallam, kayi wani abu dominka taimaki da na, shi kadai ne gare ni. 39Mugun ruhu ya kan hau kansa, ya sa shi ya yi ta magowa. Ya kan girjiza shi da karfi ya sa bakinsa ya yi ta kumfa. Da kyar ya ke rabuwa da shi, kuma ya kan ji masa ciwo ba kadan ba bayan da ya bar shi. 40Na roki almajiran ka su umurci mugun ruhun ya fita daga cikinsa, amma ba su iya ba!”

41Yesu, ya amsa, ya ce, “Ku karkatattun tsara marasa bangaskiya, har yaushe zan zauna da ku ina jimrewa da ku? “Kawo yaronka anan.” 42Sa’adda yaron yake zuwa, sai mugun ruhun ya fyada yaron a kasa, ya jijjiga shi sosai. Amma Yesu ya tsauta wa mugun ruhun, ya warkar da yaron. Sa’annan ya mika yaron wurin mahaifinsa.

43Dukansu suka yi mamaki da girman ikon Allah. Amma sa’anda suke ta yin mamaki a kan dukan al’ajiban da ya yi, ya ce da almajiransa, 44“Ku saurara da kyau a kan abin da zan gaya maku, ba da dadewa ba za a bada Dan Mutum ga mutane.” 45Amma almajiran ba su gane abin da yake nufi da haka ba, an hana su fahimta, domin kada su gane abin da ya ke nufi tukuna, kuma suna jin tsoron su tambaye shi.

46Wani lokaci, almajiran suka fara gardama a tsakaninsu game da wanene za ya zama mafi girma a cikinsu. 47Amma Yesu ya san abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya kawo dan karamin yaro ya tsaya a kusa da shi, 48sai ya ce da su, “Idan wani ya karbi dan karamin yaro kamar wannan saboda ni, dai dai yake da ya karbe ni. Idan kuma wani ya karbe ni, ya karbi wanda ya aiko ni kenan. Wanda yake mafi kankanta a cikinku, shi ne mafi mahimmanci.”

49Yahaya ya amsa yace, “Ya shugaba, mun ga wani mutum yana ba miyagun ruhohi umarni su fita daga cikin mutane da sunanka. Sai muka ce da shi ya dena yin haka saboda baya tare da mu.” 50Amma Yesu ya ce, “Kada ku hana shi yin haka, domin dukan wanda ba ya gaba da ku, yana tare da ku.”

51Sa’adda rana ta kusato da zai hawo zuwa sama, ya kudurta sosai zai tafi Urushalima. 52Ya aiki wadansu manzanni su shirya wuri dominsa kafin ya zo. Suka shiga wani kauye a cikin kauyen Samariya domin su shirya masa wuri a can. 53Amma mutanen can ba su karbe shi ba tun da ya ke Urushalima zai tafi.

54Sa’adda biyu daga cikin almajiransa, wato Yakubu da Yahaya suka ga haka, suka ce, “Ubangiji, kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama, ta hallaka su?” 55Amma, ya juya ya tsauta masu. 56Sai suka tafi wani kauye dabam.

57Da suna cikin tafiya a kan hanya, sai wani mutum ya ce da shi, “Zan bi ka dukan inda za ka tafi.” 58Yesu ya amsa masa, “Dila suna da ramuka a kasa inda za su shiga, tsuntsaye kuma suna da sheka, amma Dan Mutum ba shi da inda zai kwanta.”

59Yesu, ya ce da wani mutumin kuma, “Ka biyo ni.” Amma mutumin ya ce, “Ubangiji, ka bari in koma gida in bizine mahaifina tukuna.” 60Amma Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su bizine matattunsu; amma kai ka tafi ka yi wa mutane shelar mulkin Allah a ko’ina.”

61Wani kuma ya ce, “Ubangiji zan tafi tare da kai, amma bari in je gida inyi ban kwana da mutanena tukuna.” Yesu ya ce da shi, “Dukan wanda ya fara huda a gonarsa idan ya dubi baya, bai isa ya shiga mulkin Allah ba.”

62

Copyright information for HauULB